Shahararrun Yan Wasan Afrika: Abin da Ya Kamata Ku Sani Game da Oshoala da Nkwocha

April 2024 · 4 minute read

An saka 'yar wasan Super Falcons, Asisat Oshoala, da tsohuwar ‘yar wasan Najeriya, Perpetual Nkwocha, cikin jerin ‘yan wasa 25 da suka fi fice a Afirka a karni na 21.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zakulo 'yan wasa tare da fifitasu akan sauran abu ne mai matukar wahala, a dauki misalin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi, har yanzu ana muhawara kan wanene gwani a cikinsu.

Wa za ka zabatsa kanin Eliud Kipchoge, fitaccen dan tseren gudun fanfalaki da aka taɓa gani a duniya, da Samuel Eto'o, mai lambar yabo na zinare a Olympics? jaridar ESPN ta ba mu amsa.

'Yan wasan Najeriya a sun shiga tarihi

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure tsakanin fitacciyar jarumar Kannywood da mabiyanta a soshiyal midiya

Bisa ga bincike da kuma zabar fitattun 'yan wasan Afrika mafi shahara a karni na 21, ESPN ta ce ba za ta damu ba don an kalubalanceta kan wannan zabi da ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga Oshoala da Nkwocha, sauran ‘yan Najeriya da suka shiga jerin sun hada da taurarin Mixed Martial Art (MMA) Israel Adesanya, Kamaru Usman da kuma tauraron kwallon kafar Amurka, Osi Umenyiora.

Sai dai, a yau, za mu yi magana ne kawai kan Asisat Oshoala, Perpetual Nkwocha da kuma Kamaru Usman. Ga abin da ya kamata ku sani a kansu.

Asisat Oshoala - 'Yar wasan kwallon kafa

Asisat Lamina Oshoala, kwararriyar ‘yar wasan kwallon kafa ce ta Najeriya, wacce ke buga wasan gaba a kungiyar kwallon kafa ta mata ta Bay FC da kuma kungiyar mata ta Najeriya.

Rahoton Wikipedia ya nuna cewa ana yi wa Oshoala kallon daya daga cikin ’yan wasa mafi nagarta a fagen kwallon kafa na bangaren mata da kuma tsararrakinta.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun soki Ministan Buhari kan goyon bayan zanga zanga

An ruwaito cewa sau shida tana zama gwarzuwar 'yar kwallon mata ta Afrika, sau uku tana daga kofin UEFA na mata, kuma sau hudu tana daga kofin Sifaniya (SPD) na mata.

A Najeriya, tana cikin tawagar Super Falcons da ta lashe kofin Afirka sau uku, kuma tana shirin sake wakilcin Super Falcons a gasar Olympics ta Paris.

Perpetual Nkwocha - 'Yar kwallon kafa

Perpetua Ijeoma Nkwocha, ‘yar Najeriya ce kuma tsohuwar ‘yar wasan kwallon kafa da ta yi wasa kuma ta zama kyaftin din kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya.

Ita ce mai horas da Clemensnäs IF daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Sweden 2. A baya ta taka leda a kulob din Sunnanå SK na Sweden, inji rahoton Wikipedia.

An ce Nkwocha ta taba kasancewa gwarzuwar 'yar kwallon mata ta Afrika (zaben shekara-shekara) sau hudu, sannan sau biyar tana zama zakarar mata ta Afrika.

Kara karanta wannan

Malami ya kasafta yadda karamin ma’aikaci zai karar da albashin N70, 000 a abinci a wata

Nkwocha ta na da kwarewa a taka leda da kuma zura kwallaye wanda ya sa sunanta ya shiga cikin littattafan tarihi a matsayin ɗaya daga cikin manyan 'yan wasan ƙwallon ƙafa na mata na Afirka.

Kamaru Usman - Dan wasan dambe/kokowa

Kamarudeen Usman ya hada jinin Najeriya da Amurka, kuma kwararre a bangaren wasannin motsa jiki da fada, tsohon dan kokawa ne, kuma ya yi kwas kan kokawar gargajiya.

An haife shi a Auchi a jihar Edo a Najeriya.

A halin yanzu yana fafatawa a rukunin matsakaicin nauyi a gasar zakarun dambe ta Ultimate, inda ya taba kasancewa zakaran Welterweight UFC.

A shekarar 2021, Usman ya kasance gwarzon dan kokowa na ESPN bayan ya lallasa Gilbert Burns da salon TKO, Jorge Masvidal da salon KO da Colby Covington bayan hukuncin alkalai.

Najeriya za ta yi hayar kocin 'yan kwasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NFF ta yanke shawarar dauko hayar mai horar da 'yan wasa daga Turai domin jan ragamar tawagar Super Eagles.

Wannan na zuwa ne bayan da Super Eagles suka sha kashi a wasanni biyu jere yayin da suka gaza tabuka abin kirki a wasanni hudu karkashin Finidi George.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHDDwKyYp6aZZH53fJJubmplo52uqa3RmqmrrZ5ixqK6jLCYrJmeYq6nvsikmGaZXaOuq7HRorCaZZ%2BotbCty5pknZldo7i4u8KhmGg%3D